'Komawa ta Man City babbar dama ce'

Frank Lampard Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Dan wasan ya ce zai yi amfani da gogewarsa a Man City

Frank Lampard ya ce komawarsa Manchester City wasa aro, ba karamar dama ba ce, inda ya fara karbar horo tare da 'yan wasan kulob din ranar laraba.

Chelsea ce ta sallami Lampard bayan ya shafe shekaru 13 da kulob din a watan Yuni inda ya kulla kwantaragin shekara 2 a watan Yuli da New York City.

Dan wasan tsakiya dan Ingilan, an ba da shi aro ne ga City zuwa watan Janairu, domin sai a watan Maris ne za a fara gasar wasan kofin Afirka.

Lampard mai shekaru 36, ya ce, "Wannan wani sabon babi ne a harkar wasa na, ina farin ciki samun wannan damar da zanyi amfani da gogewa ta."