Liverpool ta dauko Manquillo aro

Javier Manquillo Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Dan kwallo na bakwai kenan da Liverpool ta dauko kenan

Kulob din Liverpool ya dauko Javier Manquillo kan kwantiragin shekaru biyu daga Atletico Madrid da zai buga mata wasanni aro.

Dan kwallon Spaniya mai shekaru 20, shi ne dan wasa na bakwai da Liverpool ta dauko a bana da suka hada da Rickie Lambert da Adam Lallana da Emre Can da Lazar Markovic da Dejan Lovren da Divock Origi.

Manquillo ya ce "Ya yi farinciki da zai bugawa Liverpool kwallo, domin tana daga cikin manyan kungiyoyi a Nahiyar Turai, kuma kowanne dan wasa zai so ya buga mata wasa".

Dan wasn ya fara buga tamaula da kulob din Real Madrid tun yana da shekaru 13 da haihuwa, daga baya ya koma Atletico Madrid.

Ya fara wasa a kwararren dan kwallo yana da shekaru 17, ya kuma buga wasanni shida a bara, ciki har da karawar da ya yi da Real Madrid a kofin Copa del Rey inda ya ji rauni a wasan.