Zambia ta nada Janza sabon kocinta

Zambia Team Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Zambiya na kokarin samun tikitin zuwa gasar cin kofin Nahiyar Afirka a badi

Kasar Zambia ta nada Honour Janza a matsayin sabon kocin tawagar 'yan wasan kasar domin maye gurbin Patrice Beaumelle wanda ya bar aiki a farkon makwan nan.

Shugaban hukumar kwallon kafar Zambiya Kalusha Bwalya ya ce "Muna da kalubale a gabanmu, amma da kwarewar Janza zai iya kaimu gaci".

"Kuma dama ce ga kocin mai horas da 'yan wasa na gida, ya nuna kwarewar da ya samu a lokacin da suka yi aiki da Herve Renard na tsawon shekaru biyar tare".

Zambiya za ta karbi bakuncin Mozambique a wasan neman shiga gasar cin kofin Nahiyar Afirka ranar shida ga watan Satumba, sannan ta bukunci Cape Verde bayan kwanaki hudu.

Chipolopolo ta maye gurbin tsohon kocinta Beaumelle wanda ya yanke shawarar komawa Ivory Coast dan aiki tare da Renard.