Kocin Zimbabwe Gorowa ya yi ritaya

Zimbabwe Team Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Kocin ya ce ba a biya shi albashin watanni bakwai ba

Kocin kasar Zimbabwe Gorowa ya yi ritaya daga aikinsa, bisa sabani da ya samu da mahukuntan kwallon kasar da batun rashin biyan albashi.

Cikin wasikar da mujallar Herald dake Zimbabwe ta wallafa, Gorowa ya ce ba a biya shi albashin watanni bakwai ba.

Ya kuma ce yana bin hukumar kwallon kafar kasar ladan wasa da ya jagoranci Zimbabwe kaiwa wasan daf da na kusa da karshe a gasar kofin Afirka ta 'yan wasan dake taka leda a gida.

Tsohon dan kwallon Zimbabwe, ya maye gurbin Klaus Dieter Pagels dan kasar Jamus a watan Yulin bara.

Gorowa ya yi rashin nasara a wasanni biyu daga cikin wasanni 17 da ya jagoranci kasar, har da rashin nasarar da suka yi a hannun Tanzaniya a wasan neman tikitin shiga kofin Nahiyar Afirka a badi.