Arsenal na jiran abokiyar karawa

Arsene Wenger Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Shekaru 14 Arsenal na kaiwa wasan zakarun Turai

Kulob din Arsenal kila ya kara da Athletic Bilbao ta Spain, a jaddawalin wasan cike gurbin shiga gasar cin kofin zakarun Turai da za a fidda ranar Juma'a.

Gunners tana daga cikin kungiyoyi biyar da suka kai wannan matsayi da za a hada su da kulob luka biyar da ba sa cikin zakaru, amma suka kai matakin neman gurbin shiga gasar.

Athletic Bilbao ce ta fidda Manchester United a gasar cin kofin zakarun Turai wato Europa League a wasan zagaye na biyu a shekarar 2011-12.

Idan an fidda jaddawalin za su fafata a wasa gida da waje daga tsakanin 19 zuwa 20 da 26 zuwa 27 na watan nan.

Sauran kungiyoyin da za su iya haduwa da Arsenal sune FC Copenhagen to Denmark ko Lille ta France ko Besiktas ta Turkiya ko kuma Standard Liege ta Belgium.

Shekaru 14 Arsenal tana zuwa gasar cin kofin Turai a jere, a bara kulob din Fernerbace ta doke da ci 5-0 a karawar da suka yi gida da waje.