John Stone ya tsawaita kwantiraginsa

John Stone Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Dan kwallon Ingila mai shekaru 20 da haihuwa

Dan kwallon Everton John Stones ya tsawaita kwantiraginsa da kulob din, domin ci gaba da buga masa wasa zuwa shekaru biyar masu zuwa.

Dan kwallon mai shekaru 20, yana daga cikin 'yan wasan da Ingila ta ware masu jiran ko ta kwana a gasar kofin duniya da aka buga a Brazil.

Stone ya bi sahun 'yan wasa Ross Barkley da Seamus Coleman a jerin wadanda suka tsawaita kwantiraginsu da kulob din.

Dan wasan ya koma Everton ne daga Barnsley a watan Fabrairun shekarar 2013, kuma nan take ya fara buga mata tamaula, harma ya buga wasanni 21, lokacin da kulob din ya kare a mataki na biyar a teburin Premier.