Za'a saurari daukaka karar Suarez

Luis Suarez Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Suarez na fatan za'a rage hukuncin da aka yanke masa

Lauyoyin Luis Suarez suna da karfin gwiwa za a rage wa dan kwallon Barcelona hukuncin hana shi wasa na watanni hudu da aka yanke masa bisa cizon dan wasan Italy zuwa watanni biyu.

Kotun daukaka kara ta 'yan wasa, za ta saurari karar da tsohon dan kwallon Liverpool din ya shigar ranar Juma'a.

Suarez, mai shekaru 27 da haihuwa, zai dawo buga wasa ranar 25 ga watan Agusta idan an rage hukuncin da aka yanke masa zuwa watanni biyu.

Fifa ce ta yanke hukuncin dakatar da Suarez buga wasa da shiga duk wata harkar kwallon kafa tsawon watanni hudu, bayan da aka same shi da laifin cizon dan kwallon Italiya Giorgio Chiellini a gasar kofin Duniya.

Lauyoyin Suarez za su kalubalanci hukuncin ne da cewa ya shafi wasan kasa da kasa ne kawai banda na kungiya.