West Ham na neman 'yan kwallo 4

Sam Allardyce Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Allardyce na son siyan 'yan kwallon kafin fara gasar bana

Kulob din West Ham na neman 'yan wasa hudu masu zura kwallo a raga, domin bunkasa 'yan kwallon da Sam Allardyce yake horaswa.

Andy Carroll yana jinyar rauni sai a watan Nuwamba zai dawo buga tamaula, shi kuma sabon dan wasa Enner Valencia da kulob din ya sayo kan kudi fan miliyan 20, ba za a fara gasar wasan bana da shi ba.

Ana alakanta Allardyce da cewa yana zawarcin Peter Crouch na Stoke City da dan kwallon Arsenal Joel Campbell da dan wasan Portugal Hugo Almeida.

West Ham ta dauko 'yan wasa shida a bana da suka hada da Mauro Zarate da dan kwallon Ecuador Enner Valencia.

David Sullivan daya daga cikin mamallakan West Ham ya ce "Enner ya fara atisaye da 'yan wasa, zai kuma fara buga kwallo a gasar cin kofin Capital One da kulob din zai buga ranar 26 zuwa 27 ga watan Agustan bana.