Manchester City ta dauki Zuculini

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Zuculini shine dan Kasar Argentina na biyar a Kulob din City

Manchester City ta tabbatar da daukar dan wasan tsakiya Bruno Zuculini

Dan wasan mai shekaru 21 ya yiwa City wasa a lokacin wasannin su a Scotland da Amurka inda suka ci wasansu na sada zumunta da suka buga da Kansas City

Zuculini ya ce ya yi farinciki sosai game da makomarsa a City

Zuculini zai buga wasan da za'a yi da Arsenal a ranar Lahadi

Zai kasance dan wasan kasar Argentina na biyar dake cikin 'yan wasan Manchester City