Liverpool ta casa Borussia Dortmund

Liverpool Friendly Hakkin mallakar hoto epa
Image caption Liverpool ta kammala wasannin atisayen bana

Kulob din Liverpool ya caskara Borussia Dortmund da ci 4-0, a wasan atisayen tunkarar gasar wasannin bana da suka kara ranar Lahadi.

Daniel Sturridge ne ya fara zura kwallo a raga, lokacin da ya samu dama ta hannun Phillippe Coutinho.

Sabon dan wasa Dejan Lovren da Liverpool ta dauko kan kudi fan miliyan 20 daga Southampton ne ya kara kwallo ta biyu daga bugun kusurwa da Steven Gerrard ya bugo.

Coutinho ne ya kara kwallo ta uku a raga, kafin Jordan Henderson ya zura kwallo ta hudu a ragar Borussia Dortmund.

Liverpool karkashin koci Brendan Rodgers wadda ta kare matsayi na biyu a teburin Premier bara, za ta fara karawa da Southampton a gasar cin kofin Premier bana ranar Lahadi.