Gasar Premier Nigeria wasannin mako 22

Nff
Image caption wasannin mako na 22 da za'a fafata a filaye da dama a Nigeria

Yau ne za'a shiga mako na 22 a gasar cin kofin Premier Nigeria, inda za'a kara a filayen wasanni daban daban a fadin kasar.

Cikin wasan da za'a fafata Giwa Fc zata karbi bakuncin Dolphins ta Fatakwal, Nembe City zata ziyarci Warri Wolves, sai Akwa United ta barje gumi da Nasarawa United.

Kulob din Lobi Stars zai karbi bakuncin Sharks, sai Kano Pillars wacce take matsayi na daya a teburi ta ziyarci Sunshine Stars ta Akure, da kuma karin battar mayaka tsakanin Abia Warriors da El-Kanemi Warriors a garin Abia.

A garin Owerri Heartland zata kai ruwa rana tsakaninta da Crown Fc ta Oshogbo, kungiyar Kaduna United na garin Taraba a fafutukar neman maki tsakaninta da Taraba Fc, da kuma wasa mai zafi na gani na fada tsakanin Enugu Rangers da Enyimba International ta Aba.

Ga jaddawalin wasannni da za su kara tsakaninsu:

Giwa FC vs Dolphins FC Warri Wolves vs Nembe City Enugu Rangers vs Enyimba Akwa United vs Nasarawa United Heartland FC vs Crown FC Lobi Stars vs0 Sharks Sunshine Stars vs Kano Pillars Abia Warriors vs El-Kanemi Warriors Taraba FC vs Kaduna United

Bayelsa United vs Gombe United