Sunshine Stars ta doke K/Pillars 3-0

Kano Pillars Hakkin mallakar hoto Kano Pillars Web Site
Image caption Har yanzu Kano Pillars ce ke matsayi na daya a teburi

Kungiyar Sunshine Stars ta Akure ta doke kulob din Kano Pillars da ci 3-0 a gasar cin kofin Premier wasannin mako na 22 da suka fafata ranar Lahadi.

Sauran sakamakon wasannin sun hada Warri Wolves data lashe Nembe Ciry da ci daya mai ban haushi, wasa tsakanin Giwa Fc da Dolphins tashi suka yi kunnen doki.

Gombe United har gida ta doke Bayelsa United da ci daya mai ban haushi, inda karawa tsakanin Enugu Rangers da Enyimba ta Aba suka tashi wasa kunnen doki, sai Taraba Fc data doke Kaduna United da ci 2-0

Har yanzu Kano Pillars ce ke matsayi na daya a teburi bayan wasannin mako na 22 da maki 37, sai Abia Warriors da maki 36 a matsayi na biyu, inda Nasarawa United keda maki 35 a mataki na uku.

Ga sakamakon wasannin mako na 22 da suka buga:

Giwa FC 1 vs 1 Dolphins FC Warri Wolves 1 vs 0 Nembe City Enugu Rangers 1 vs 1 Enyimba Akwa United 0 vs 0 Nasarawa United Heartland 1 0 vs Crown FC Lobi Stars 1 vs 0 Sharks Sunshine Stars 3 vs 0 Kano Pillars Abia Warriors 2 vs 0 El-Kanemi Warriors Taraba FC 2 vs 0 Kaduna United Bayelsa United 0 vs 1 Gombe United