Klose ya yi ritayar buga wa Jamus wasa

Miroslav Klose Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Klose ya yi murna da gudunmawar da ya bai wa Jamus

Miroslav Klose wanda yafi kowawanne dan wasa a Jamus yawan zura kwallo a raga ya yi ritaya daga buga wa kasar Tamaula.

Dan wasan mai shekaru 36 da haihuwa dan kwallon Lazio, ya taimakawa kasarsa lashe kofin duniya, har ma ya kafa tarihin wanda yafi yawan jefa kwallo a gasar kofin Duniya.

Klose, ya zura kwallaye 71 a wasanni 137 da ya bugawa Jamus, kuma dan wasa da ya kasance na uku da ya zura kwallo a kofin Duniya karo hudu da ya halarta, ya zura kwallaye 16 a raga Jumulla.

Haifaffen kasar Poland Klose ya ce "Ya yi matukar farin ciki da ya bada gudunmawarsa da Jamus ta samu nasara a kwallon kafa".

Dan wasan ya shafe shekaru 13 yana bugawa kasarsa wasa, kuma shi ne dan kwallo na biyu da yi yi ritayar buga wasa, bayan Kyaftin din tawagar kasar Philipp Lahm tun bayan kofin Duniya.