Togo na son a dage wasanta da Guinea

Ebola Virus Hakkin mallakar hoto Science Photo Library
Image caption Togo na fargabar kamuwa da cutar Ebola a Guniea

Kasar Togo ta nemi a dage karawar da za tayi da Guinea a wasan neman tikitin shiga gasar kofin Nahiyar Afirka da za su yi a watan gobe bisa fargabar kamuwa da cutar Ebola.

Karawar da hukumar kwallon kafar Afirka (CAF) ta shirya da za su fafata a watan Satumba daga ranar 5 zuwa 6, kuma shi ne wasan farko na cikin rukunin.

Sama da mutane 300 ne suka mutu a Guinea saboda cutar Ebola, inda nan ne cutar ta fara bulla daga baya ta watsu zuwa wasu makwabtanta da suka hada da Liberia da Saliyo.

Hukumar kwallon kafar Togo (TFF) ta ce, za ta jira shawarar da gwamnatin kasar za ta yanke kan ziyartar tawagar 'yan wasan zuwa Guninea.

Hukumar ta ce "Ta damu matuka kan yadda cutar Ebola ke yaduwa".