Kano Pillars za ta fafata da Rangers

Kano Pillars Hakkin mallakar hoto Kano Pillars Web Site
Image caption Pillars rashin nasara ta yi da ci uku da nema a karshen makon da ya wuce

Kano Pillars za ta karbi bakuncin Enugu Rangers a gasar cin kofin Premier ta Nigeria wasannin mako na 23 ranar Laraba.

Pillars wadda take matsayi na daya a teburin Premier, ta sha kashi a hannun Sunshine Stars da ci uku da nema, inda Rangers ta buga kunnen doki tsakaninta da Enyimba a wasannin mako na 22 da suka kara ranar Lahadi

Sauran wasanni sun hada da kai ruwa tsakanin Kaduna United da Akwa United, sai Nasarawa United da za ta karbi bakuncin Bayelsa United.

Kungiyar Enyimba za ta kara da Warri Wolves, sai Taraba United da za ta ziyarci El-Kanemi Warriors a jihar Kano.

Har yanzu Kano Pillars ce ke matsayi na daya da maki 37 daga cikin wasanni 22 da ta buga, inda Abia Warriors mai maki 36 ke matsayi na biyu, Nasarawa na mataki na uku da maki 35.

Ga jerin jaddawalin wasannin mako na 23.

Kano Pillars vs Enugu Rangers Enyimba vs Warri Wolves Kaduna United vs Akwa United Nembe City vs Abia Warriors Giwa FC vs Sunshine Stars Nasarawa United vs Bayelsa United Sharks vs Heartland FC El-Kanemi Warriors vs Taraba FC Dolphins FC vs Crown FC Gombe United vs Lobi Stars