Karabukspor ta kammala daukar Akpala

Joseph Akpala Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Akpala bai bata lokacin yanke amincewa komawa kulon din ba

Dan kwallon Nigeria Joseph Akpala, ya koma kulob din Karabukspor na Turky dungurungum bayan da ya buga mata wasa aro a kakar wasan bara.

Dan wasan mai shekaru 27 da haihuwa, ya taimakawa kungiyar samun tikitin shiga gasar cin kofin zakarun Turai a bara, wanda ya koma kungiyar daka Werder Bremen kan kwantiragin shekaru uku.

Akpala, wanda ya zura kwallaye 6 daga wasanni 14 da ya buga ya ce "Lokacin da kulob din ya nemi amincewa ta na buga masa wasa, ban bata lokaci wajen rattaba kwantiragi ba".

Dan wasan ya bugawa Najeriya wasa a gasar zakarun Nahiyoyi wato Confederatins Cup da aka kammala a Brazil a shekarar 2013.

Akpala ya koma Werder Bremen kan kwantiragin shekaru hudu a shekarar 2012 daga kungiyar Club Brugge ta Belgium.