Bale na fatan lashe kofuna shida a bana

Gareth Bale Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Bale na harin lashe kofuna shida da Madrid a bana

Dan kwallon Real Madrid Gareth Bale, na fatan lashe kofuna shida da kulob din a kakar wasan bana.

Dan wasan mai shekaru 25 da haihuwa, zai buga karawar da za suyi da Sevilla a gasar cin kofin Uefa Super Cup a filin wasa na Cardiff.

A kakar bana Real Madrid na fatan lashe kofin zakarun Turai wato Champions League da La Liga da Copa del Rey da kofin zakarun kungiyoyin na Duniya wato Fifa Club World Cup da kuma Supercopa de Espana.

Bale ya ce tuni ya saba da kwallo a Bernabeau tamkar yana gida, kusan shekararsa guda da komawa kulob din daga Tottenham kan kudi sama da fan miliyan 85.

Gasar Super Cup da za su fafata, ana karawa ne tsakanin wacce ta lashe kofin zakarun Turai wato Champions League wadda itace Real Madrid da kuma wacce ta lashe kofin Europa League wato Sevilla.