Real Madrid ta lashe kofin Super Cup

Real Madrid
Image caption Real Madrid ta lashe kofin Uefa Super Cup

Kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid ta lashe kofin Uefa Super Cup, bayan da ta doke Sevilla da ci biyu da nema a karawar da suka yi a birnin Cardiff.

Ronaldo, wanda ya fara wasan tare da sabbin yan kwallon da kulob din ya dauko a bana James Rodriguez da Toni Kroos, shi ne ya fara zura kwallo a raga mintuna 30 da fara wasa.

Dan wasan ya kara kwallo ta biyu a raga a mintuna na biyar da dawowa daga hutun rabin lokaci, bayan da ya samu kwallo ta hannun Karim Benzema.

Tun kafin karawar Gareth Bale ya bayyana fatansa na lashe kofuna shida a bana da suka hada da La Liga da Copa del Rey da Fifa Club World Cup da Supercopa na Espana.

Ga sunayen 'yan wasan da suka buga wa Real Madrid:

Casillas, Carvajal, Pepe, Sergio Ramos, Fabio Coentrao, Kroos, Rodriguez, Modric, Bale, Benzema, Ronaldo. Subs: Navas, Varane, Marcelo, Arbeloa, Di Maria, Isco, Illarramendi.

Ga sunayen 'yan wasan da suka buga wa Sevilla:

Beto, Coke, Pareja, Fazio, Fernando Navarro, Alex Vidal, Krychowiak, Carrico, Vitolo, Suarez, Bacca. Subs: Barbosa, Diogo Figueiras, Reyes, Jairo, Iborra, Aspas, Luismi.

Alkalin wasa: Mark Clattenburg (England)