Dortmund ta doke Munich a Super Cup

Borussia Dortmund Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Borussia Dortmund ta lashe Super Cup na Jamus

Kungiyar kwallon kafa ta Borussia Dortmund ta doke Bayern Munich da ci 2-0 a gasar Super Cup na Jamus.

Henrikh Mkhitaryan na Dortmund ne ya fara zura wa Munich kwallo a raga kafin daga baya Pierre-Emerick Aubameyang ya kara kwallo ta biyu a raga da ka.

Bayern ce ta lashe kofin Bundesligar Jamus a bara da tazarar maki 19, kuma ta doke Dortmund a wasan karshe na cin kofin kalubale.

Tsohon dan kwallon Dortmund Robert Lewandowski, ya buga wasansa na farko a Munich, sabon kulob din da ya koma.

Ranar Juma'a 22 ga watan Satumba za a fara gasar cin kofin Bundesliga, kakar wasan bana 2014-15.

Borussia Dortmund: Langerak; Piszczek, Papastathopoulos, Ginter, Schmelzer (Durm 45); Kirch (Bender 85), Kehl; Mkhitaryan, Hoffman, Immobile; Aubameyang (Ramos 63).

Bayern Munich: Neuer: Boateng, Martinez (Dante 31), Alaba; Hojbjerg (Gotze 59), Rode, Gaudino, Bernat; Shaqiri, Lewandowski, Muller (Lahm 45).