Gasar Premier Ingila ta bana 2014/15

Mancity winner
Image caption Shin wa zai lashe kofin Premier Ingila kakar wasan bana

Bayan kammala Gasar cin kofin duniya, masu sha'awar kwallon kafa a duniya sun kuma mayar da hankali kan Gasar Premier ta Inghila wadda za'a fara kakar bana 2014-15 ranar Asabar.

Yayin da Gasar Premier ke ikrarin ita ma'abota kwallon kafa suka fi kallo a kan sauran gasar wasanni, sai ga shi Gasar La Liga ta Spaniya da Bundesliga ta Jamus na neman zama barazana a gare ta a yankunan Afirka da Asiya har da ma Gabas ta Tsakiya.

Sashen wasanni na BBC ya tsakuro wasu kulob-kulob da 'yan wasa masu horas da su da za a mayar da hankali a kansu a kakar wasanni na bana tare da jin ra'ayin magoya baya da masana harkar kwallo da marubuta a duniya kan wasannin.

Kulob-kulob da za a kalla

Manchester United: Bayan kammala kakar bara, kulob din ya kare a matsayi na bakwai karkashin jagorancin David Moyes wanda shi ne sakamako mafi muni da kulob din ya taba samu a Gasar ta Premier. Magoya bayan kulob din a duniya za su sa ido don ganin yadda Manchester za ta sake dawo da martabarta tare da sabon koci Louis van Gaal.

Liverpool: Liverpool na daga cikin gaggan kulob-kulob da suka kashe kudi a bazara inda suka sayar wa da Bercelona dan wasan gaba Luis Suarez kan kudi fam miliyan 75.

Duk da cewa ita ce ta biyu a karshen kakar ta bara, inda take bin mai rike da kofi watau Manchester City, kocin kulob din zai so ace Liverpool ta kara ci gaba ko da ba gudunmawar Luis Suarez.

Kocin ya kuma yi hanzarin yin amfani da kudin da aka sayar da Suarez wajen sayo 'yan wasa bakwai a wannan bazarar. Magoya bayan kulob din za su yi farin ciki suga cewa kulob din ya kara karfi, amma wasunsu da dama na nuna damuwa dangane da sake maimaita kuskuren da kulob din Tottenham ya yi na sayan 'yan wasa da yawa da suka zama madadin Gareth Bale ya koma Real Madrid.

Mai yiwu wa kulob din ya sake neman wani dan wasan gaba da zai maye gurbin Suarez wanda ya ci kwallaye 31 a bara, inda ya taimaka musu a nasarar da kulob din ya samu.

Manchester City:

Bayan sun dauki kofin Premier a karo na biyu cikin shekaru uku, Manchester City ta fara kakar bana da 'yan wasan da aka saba ganin su, inda ta rike tawagar 'yan wasan da suka ci mata kofi.

City, ta kara sababbin 'yan wasa da suka hada da dan wasan tsakiyar Brazil Fernando da dan wasan baya na Faransa Eliaquim Mangala da kuma Bacary Sagna wadanda ake sa ran za su taka rawa a fafatawar da za a yi a Gasar ta Premier. Haka kuma kocin kulob din Manuel Pellegrini, na burin sake zama zakara a karshen Gasar.

Chelsea: Chelsea ita ma ta sayo wasu fitattun 'yan wasa a kokarin da kocin kulob din Jose Mourinho ke yi na sake gina kulob din bayan tafiyar Frank Lampard da Ashley Cole da Demba Ba da David Luiz da kuma Samuel Eto'o. Shahararrun 'yan wasa kamar su Diego Costa da Cesc Fabregas na daga cikin wadanda za su taka leda a tawagar ta Chelsea wadanda suka yi faduwar bakar tasa a Gasar cin kofin duniya bayan da suka kasa fitowa daga rukuninsu.

Arsenal:

Kulob din Arsene Wenger ya kawo karshen kishirwar kofi da yake fama da ita lokacin da ya dauki kofin FA a kakar bara. Haka kuma magoya bayansa na sa idon samun ci gaba a wannan karo. Amma nasarar da kulob din ya samu kan Manchester City inda ya lallasa ta da ci 3-0 ya nuna cewa sun fara kakar da kafar dama.

Magoya bayan Arsenal sun sa ido don ganin kocin kulob din Wenger ya yi amfani da makudan kudin da Arsenal ke da shi. Sai dai mai yiwuwa sayan Alexis Sanchez daga Bercelona kan kudi fam miliyan £35 na iya faranta musu rai ganin yadda kwararren dan wasan gaban zai kara karfafa gaban Arsenal da wasu dabaru.