AC Milan ta dauko Golan Madrid Lopez

Diego Lopez Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Golan ya koma wasa a Serie A, bayan da ya buga La Liga

Kulob din AC Milan ya dauko golan Real Madrid Diego Lopez, sai dai kungiyar ba ta fayyace kudin da ta dauko dan kwallon ba.

Lopez, mai shekaru 32 da haihuwa ya koma Real Madrid ne a watan Janairun 2013, lokacin da golan Madrid Iker Casillas ya gamu da karaya a hannunsa.

Dan wasan Spaniya ya ci gaba da kama wa Madrid kwallo duk da samun saukin da Casillas ya yi, har ma ya kama wasanni 52 a gasar cin kofin La Liga.

Madrid ta dauko golan Costa Rica Keylor Navas daga Levante a bana, dalilin da Lopez ya samu damar barin kulob din zuwa buga gasar Seria A na Italiya.

Madrid ta sanar a shafinta na Intanet "Tana yi wa golan godiya da fatan alheri, bisa yadda ya ba da gudunmawarsa a ci gaban kulob din".