Aguero ya kulla sabon kwantiragi

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Aguero ya buga wa Man City wasanni 122 kuma ya ci kwallaye 75.

Dan wasan Manchester City Sergio Aguero ya sanya hannu a sabon kwantiragi na shekara biyar da zakarun Premiern.

Dan wasan mai shekaru biyar, ya bi sahun Samir Nasri d Aleksandar Kolarov da Vincent Kompany da David Silva, wajen sabunta kwantiragin da zai kai shi har shekara ta 2019 a kungiyar.

Aguero ya yi suna saboda kwallon da ya ci wa City a cikin minti na karshe, wadda ta ba su damar dukar kofin Premier a ranr karshe t kakar wasan ta 2011/12.

Dan wasandan kasar Argentina, ya ce ya ji dadin kakar da ta wuce, amma bai gamsu da kofunan Premier biyu kawai ba.

Karin bayani