An tabbatar da hukuncin Suarez

Luis Suarez Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Suarez zai iya shiga harkokin wasan kwallon kafa

Kotun daukaka karar wasanni ta tabbatar da hukuncin dakatarwar da aka yi wa Luis Suarez dan kwallon Uruguay, amma zai iya atisaye da Barcelona.

Lauyan Suarez ya kalubalanci hukuncin da Fifa ta yanke bisa cizon dan kwallon Italiya Giorgio Chiellini da ya yi a gasar kofin duniya da cewa, hukuncin ya yi tsauri.

Suarez, mai shekaru 27 zai fara buga wa Barcelona wasa daga 26 ga watan Oktoba, lokacin da za su kara da Real Madrid.

Dan wasan zai dawo harkokin kwallon kafa, zai kuma iya buga wa Uruguay wasannin sada zumunci, ban da manyan gasar kwallon kafa guda tara, zai kuma halarci filayen wasanni da kuma yi wa kamfunoni tallace-tallace.

Lauyan Suarez ya ce hukuncin da aka yanke na nufin dan wasan zai buga wa Uruguay wasan sada zumunci da za ta kara da Japan da Korea ta kudu da Saudi Arabia a watan Satumba da Oktoba.

Zai kuma iya buga wa Barcelona wasan atisaye da kulob din zai buga da kungiyar Leon na Mexico ranar Litinin.

Fifa ce ta yanke hukuncin dakatar da Suarez buga wasa da shiga duk wata harkar kwallon kafa tsawon watanni hudu, bayan da aka same shi da laifin cizon dan kwallon Italiya Giorgio Chiellini a gasar kofin Duniya.