Kenya na zargin sayar da wasa

Kenya FKF Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Kenya na zargin an sayar da wasanta da Lesotho

Hukumar kwallon kafar Kenya na zargin sayar da wasan da Lesotho ta yi waje da ita a karawar neman tikitin shiga gasar kofin Nahiyar Afirka.

A wani jawabi da hukumar kwallon Kenya ta fitar ta ce tana zargin doke ta da a ka yi a wasan farko da ci daya mai ban haushi da abin banbarakwai.

Ta kara da cewa "Za ta binciki lamarin, kila an yi cinikin wasan ne ko kuma zagon kasa aka yi mata".

Tuni hukumar ta nada kwamitin mutane bakwai da zai mika rahotansa nan da makwanni uku masu zuwa.

Kwamitin zai binciki masu horas da tawagar 'yan kwallon kasar, da yadda suka dunga sada sakwanni tsakaninsu, da duk wani lamari da zai fayyace gaskiyar zargin.