Nigeria ce ta uku a taka leda a Africa

Nigeria Super Eagles Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Nijeriya ta koma mataki na uku a iya kwallo a Afirka

Nigeria ta dare matsayi na uku a jerin kasashen da suka fi iya taka kwallo a nahiyar Afirka, a sakamakon da hukumar Fifa ta fitar na watan Yuli.

Super Eagles ta gusa zuwa mataki na ukun ne a Afirka, sannan ta koma matsayi na 34 a jerin kasashen da suka fi iya taka leda a Duniya.

Najeriya ta samu kai wa wannan matsayin ne bisa kokarin da tawagar 'yan kwallon kasar suka yi a gasar cin kofin duniya, in da suka kai wasan zagaye na biyu.

Kasar Cape Verde ta yi kasa daga mataki na biyar inda ta koma na 15 a Afirka, sannan ta 75 a Duniya.

Ga jerin kasashe 10 na farko da suka fi iya taka leda a Afirka da Duniya

1. Algeria (24)

2. Ivory Coast (25)

3. Nigeria (34)

4. Egypt (36)

5. Ghana (38)

6. Tunisia (42)

7. Guinea (51)

8. Cameroon (53)

9. Burkina Faso (58)

10. Mali (60)