Zaben gwarzon 'yan kwallon Turai

Hakkin mallakar hoto PA
Image caption Golan ya na cikin yan takarar gwarzon 'yan kwallon bana na Turai

Golan Bayern Munich Manuel Neuer da Arjen Robben da dan kwallon Real Madrid Cristiano Ronaldo, na daga cikin 'yan wasan da za a zabi wanda ya fi fice a Nahiyar Turai.

'Yan kwallon uku dai 'yan jaridu ne suka zabo su bisa kokarin da 'yan wasan suka yi a kakar bara, inda ake sa ran gudanar da zaben gwarzon banar ranar 28 ga watan Agustan nan.

Golan Jamus Neuer ya taimaka wa kasarsa lashe kofin duniya da aka kammala a Brazil, ya yin da Robben ya zura kwallaye 21 da Bayern da kuma kwallaye uku ga Netherlands a gasar cin kofin Duniya.

Dan kwallon Portugal Ronaldo ya taimaka wa Real Madrid lashe kofin zakarun Turai in da ya zura kwallaye 17.

Za a fidda gwarzon ne na bana da 'yan jaridu za su fitar a lokacin da za a raba jaddawalin wasannin rukunin gasar cin kofin zakarun Turai.