West Ham ta dauki Sakho

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Sakho shi ne dan wasan gaba na uku da ya koma West Ham

West Ham ta kulla kwantaragi da dan wasan gaban FC Matz ba tare da bayyana farashi ba.

Dan wasan mai shekaru 24, dan Kasar Senegal, ya koma Upton Park bayan kulla yarjejeniyar kwantaragin shekaru hudu.

Cin kwallaye 43 da ya yi bara a gasar ta taimaka masa samun ci gaba a gasar Faransa.

Sakho shi ne dan wasan gaba na uku da ya koma West Ham a wannan bazarar bayan zuwan Mauro Zarate dan kasar Argentina da kuma Enner Valencia na kasar Ecuador.

Sakho ya fada wa West Ham TV cewa, "Hakika ina son wasannin gasar Premier, na kuma sha mafarkin zuwa don yin wasa a daya daga cikin kulob- kulob da keturai, sai ga shi yanzu West Ham ta bani wannan dama da na ke nema, na kuma karba ba tare da bata lokaci ba."