Suarez zai buga wa Barcelona wasa

Luis Suarez Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Barcelona za ta gabatar da Suarez gaban magoya bayanta

Kocin Barcelona Luis Enrique ya ce sabon dan kwallon da kulob din ya dauko Luis Suarez zai buga karawar da kungiyar za ta yi da Leon a wasan sada zumunci ranar Litinin.

Makon da ya gabata ne dai kotun daukaka karar wasanni ta Duniya ta tabbatarwa da Suarez hukuncin da aka yanke masa na hana shi buga wasanni har tsawon watanni hudu.

Dan kwallon Uruguay mai shekaru 27 da haihuwa, zai iya yin atisaye da buga wasannin sada zumunci da yiwa kamfanoni tallace-tallace.

Suarez ya yi atisaye da 'yan wasan Barcelona karo biyu, wanda rabonsa da taka leda tun lokacin da ya ciji dan kwallon Italiya Giorgio Chiellini a gasar cin kofin Duniya da aka kammala a Brazil.

Dan wasan zai yi zaman hukuncin rashin buga wasanni takwas da suka rage daga wasanni tara da aka yanke masa na buga gasar wasannin kasa da kasa, amma zai iya buga wa kasarsa wasan sada zumunci.

Ana kuma sa ran Suarez zai buga wa Barcelona wasan farko a gasar La Liga ranar 26 ga watan Oktoba lokacin da za su kara da Real Madri.

A ranar Litinin ne ake sa ran kulob din Barcelona zai gabatar da Suarez ga magoya bayan kungiyar ta Spaniya.