AFCON: Caf ta kori Rwanda

CAF Nation Cup
Image caption CAF ta kori Rwanda daga shiga wasan neman tikitin shiga gasar badi

Kwamitin ladabtarwa na Hukumar Kwallon Kafar Afirka (CAF) ya dakatar da kasar Rwanda daga buga wasannin neman tikitin zuwa gasar cin kofin Nahiyar Afirka da za a kara a badi

Hukuncin ya biyo bayan korafin da hukumar kwallon Congo ta shigar gabanta kan shekarun haihuwar dan wasan Rwanda Birori Dady.

Dady ya buga karawar farko a wasan zagaye na biyu da kasashen biyu suka fafata a Pointe-Noir.

Congo ta yi korafin cewa Dady, wanda yake taka leda a AS Vita Club ta Kinshasa yana da sunaye da shekaru da suka banbanta a passport dinsa.

CAF ta saurari korafin da Congo ta shigar da jawaban Rwanda da kuma jin ba asin dan wasan ranar 11 ga watan Agusta a hedikwatar hukumar da ke Cairo.

Hukumar ta ce dan wasan yana amsa sunan Etekiama Agiti Tady a tawagar 'yan wasan Rwanda, sannan shekarunsa na haihuwa sun bambanta.