Warri Wolves ta doke Kano Pillars 2-1

Kano Pillars Hakkin mallakar hoto Kano Pillars Web Site
Image caption Har yanzu Pillars ce ke matsayi na daya a teburi

Kulob din Warri Wolves ya doke Kano Pillars da ci 2-1 a gasar cin kofin Premier Nigeria wasannin mako na 24 da aka ci gaba da karawa a filaye daban-daban ranar Lahadi.

Sauran sakamakon wasanni sun hada da Akwa United data doke El Kanemi Warriors da ci daya mai ban haushi, itama Lobi Stars haka ta doke Nasarawa United da ci daya da nema, wasan hamayya tsakanin Abia Warriors da Enyimba tashi suka yi kowannensu ya zura kwallo uku a raga.

Bayelsa United tun a ranar Asabar ta doke Kaduna United da ci 3-0, wanda karawa tsakanin Sunshine Stars da Dolphins suka tashi wasa babu ci.

Har Yanzu Kano Pillars tana matsayi na daya da maki 40 a teburi, bayan buga wasan mako na 24, Nasarawa United ma na matsayinta na biyu da maki 38, yayinda Dolphins ta hada maki 38 ta kuma rike kambunta na matsayi na uku.

Ga sakamakon wasannin mako na 24:

Asabar 16 Agusta 2014 Bayelsa United 3 - 0 Kaduna United Sunshine Stars 0 - 0 Dolphin Lahadi 17 Agusta 2014 Abia Warriors 3 - 3 Enyimba FC Akwa United 1 - 0 El-Kanemi Warriors Crown FC 2 - 0 Sharks Enugu Rangers 1 - 0 Giwa FC Heartland 2 - 0 Gombe United Lobi Stars 1 - 0 Nasarawa United Taraba FC 1 - 1 Nembe City FC Warri Wolves 2 - 1 Kano Pillars