Man City ta doke Newcastle da ci 2-0

Man City Win Hakkin mallakar hoto reauters
Image caption Man City ta fara kare kambunta da kafar dama

Kulob din Manchester City zakarar kofin Premier bara ya fara gasar bana da kafar dama, inda ya doke Newcastle United har gida da ci 2-0 a karawar da suka yi ranar Lahadi.

Tun farko Newcastle ce ta dunga kai kora gidan City, amma kuma aka zura mata kwallo a raga da David Silva ya yi bayan ya samu tamaula daga bugun agara da Edin Dzeko ya bugo masa.

Dan kwallon City da ya shigo fili sauyin dan wasa Aguero ne ya zura ta biyu a raga, bayan da golan Newcastle Tim Krul ya tare bugun farko da dan wasan ya yi masa, kwallon ta sake komawa kafarsa inda ya zura ta a raga.

Dzeko dan wasan City ya samu damar zura kwallo a raga, nan ma Krul ya hana ta shiga, ya kuma hana kwallon Samir Nasri shiga raga.

Mai tsaron bayan Newcastle Paul Dummett da Ayoze Perez sun kai munanan hare-hare amma kwallayen suka bude da yawa.