'Ba a ban isasshen lokaci a United ba'

David Moyes Hakkin mallakar hoto EPA
Image caption Kocin ya so a bashi cikakken lokacin a United

Tsohon kocin Manchester United David Moyes ya ce ba a bashi isasshen lokaci a kungiyar ba, kafin a sallame shi daga aikin.

Kocin, dan kasar Scotland ya gaji horas da United a hannun Sir Alex Ferguson a watan Yulin shekarar 2013, aka kuma sallame shi cikin watan Afirilu, lokacin da kulob din ke matsayi na bakwai a teburin Premier.

Moyes ya shaidawa Mujallar Mail ta ranar Lahadi cewa "Ban ji dadi da na rasa aiki na ba, domin ina da tabbacin za mu samu nasarori da dama a kulob din a gaba, ban jin an ba ni cikakken lokacin da zai auna kwazo na ko rashin haka".

Kocin ya koma United ne daga Everton bayan da ya horas da kungiyar tsawon shekaru 11 a Goodison Park, inda ya karbi Sir Alex Ferguson, wanda ya yi kocin United tsawon shekaru 26.

United ta buga wasan farko a gasar cin kofin Premier bana da Swansea ranar Asabar, inda aka doke ta da ci 2-1 a filin Old Trafford.