'Duk Runtsi za mu gasar zakarun Turai'

Arsene Wenger Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Shekaru 16 Arsenal na halartar gasar zakarun Turai a jere

Arsene Wenger kocin Arsenal ya ce komai wuya komai runtsi za su samu tikitin shiga gasar cin kofin zakarun Turai na bana.

Gunners, wadda ta je gasar zakarun Turai shekaru 16 a jere, za ta ziyarci kasar Turkiya don karawa da Besiktas a wasan farko.

Wenger ya ce "mun kagu mu buga gasar cin kofin zakarun Turai na bana, mun latsa mun ga jini domin mun san mahimmancin gasar".

Arsenal ta doke Crystal Palace da ci 2-1, a gasar cin kofin Premier da suka kara ranar Asabar.

Besiktas doke Feyenoord ta yi a wasannin zagaye na biyu na neman tikitin shiga gasar, inda Demba Ba ya zura kwallaye uku a raga.

A bara Arsenal sai da ta doke kulob din Turkiya Fenerbahce, sannan ta samu gurbin shiga gasar zakarun Turai.