'Liverpool za ta kai ga ci ko ba Suarez'

Daniel Sturridge Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Sturridge na fatan Liverpool ta lashe kofin Premier bana

Dan kwallon Liverpool Daniel Sturridge ya ce kulob din ya kara karfi a gasar wasan bana duk da Luis Suarez wanda ya fi kowa yawan zura kwallo a gasar bara ya bar kungiyar.

Liverpool ta doke Southampton da ci 2-1 a karawar wasan farko na cin kofin Premier bana da suka buga ranar Lahadi a Anfield.

Sturridge ya ce " Liverpool ta kara karfi duk da ba sa tare da Suarez, hakika sun yi rashin dan kwallon domin zakakuri ne mai jajurcewa kuma kwararre".

Suarez ya zurawa Liverpool kwallaye 31 daga cikin manyan gasar wasanni 33 da ya bugawa kulob, kafin daga baya ya koma kulob din Barcelona kan kudi fan milyan 75.

Kocin Liverpool Brendan Rodgers ya ce, Suarez ya kira shi ta wayar sadarwa da safiya, ya kuma yi masa murnar doke Southampton da yi wa kungiyar fatan alhere a wasanninta na gaba.

Ga jerin 'yan wasan da Liverpool ta dauko a bana:

Javier Manquillo, daga Atletico Madrid Divock Origi, daga Lille kan kudi fan miliyan 10. Alberto Moreno, daga Sevilla kan kudi fan miliyan 12. Rickie Lambert, daga Southampton kan kudi fan miliyan 4. Adam Lallana, daga Southampton kan kudi fan miliyan 25. Emre Can, daga Bayern Leverkusen kan kudi fan miliyan 10. Lazar Markovic, daga Benfica kan kudi fan miliyan 20. Dejan Lovren, Southampton kan kudi fan miliyan 20.