NFF: Aminu Maigari ya koma aikinsa

Aminu Maigari Hakkin mallakar hoto getty
Image caption Shugaban ba ya sha'awar sake tsayawa takara karo na biyu

Shugaban hukumar kwallon kafar Nigeria (NFF) Aminu Maigari ya koma aiki, bayan da kwamitin amintattu na hukumar ya dakatar da shi kusan wata guda da ya gabata.

Kwamitin ya dakatar da Maigari bisa zarginsa da kashe kudaden hukumar ba ta hanyar da ya kamata ba.

Mataimakin sakataren Fifa Markus Kattner ne ya rubutawa NFF wasika da cewar korar Maigari daga mukaminsa an karya ka'idojin hukumar, ya kamata a bi yadda doka ta tsara.

Maigari ya ce lokacin da ya shiga office ranar Litinin"ya kamata mu hada kan mu don ciyar da kasa gaba, mukan samu sabani a tsakaninmu, amma mu mance da abin da ya faru a baya".

Kattner ya umarci Maigari da ya jagoranci zaben hukumar da za ta gudanar ranar 26 ga watan Agusta da kwamitin ya zabi garin Warri dake Delta don gudanar da zaben.

Maigari bai nuna alamun zai sake tsayawa takara a karo na biyu ba, domin bai mayar da takardar neman zama dan takara da ya karba a baya ba.

Mike Umeh da Chris Giwa ne aka tantance cikin wadanda suke zawarcin shugabancin hukumar NFF.