Bale zai buga karawa da Atletico

Gareth Bale Hakkin mallakar hoto real madrid on twitter
Image caption Bale ya ce kofuna shida ya ke harin lashe wa a bana

Dan kwallon Real Madrid Gareth Bale ka iya samun sauki daga raunin da ya ji domin buga wasan da kulob din zai yi da Atletico Madrid a gasar Super Cup ta Spaniya.

Dan kasar Wales bai yi atisaye da 'yan wasan kulob din ba ranar Juma a, amma ya halarci atisayen ranar Lahadi.

Athletico Madrid ce za ta fara karbar bakuncin Madrid a filin wasanta na Vicente Calderon ranar Talata, kafin a buga wasan zagaye na biyu a Bernabeu ranar Juma a.

Tuni Real Madrid ta dauki Super Cup na Turai bayan da ta doke Sevilla da ci 2-0 a birnin Cardiff.

Kocin Madrid Carlo Ancelotti ya sanar da cewa golan kungiyar Iker Casillas ne zai shiga raga, Keylor Navas zai zauna a benci don jiran ko ta kwana.

Barcelona ce ta lashe Super Cup na Spaniya da ake karawa tsakanin zakaran kofin La Liga da wadda ta tauki kofin kalu bale, bayan da ta samu nasara a kan Atletico bara.