Besiktas da Arsenal sun tashi wasa 0-0

Besiktas vs Arsenal Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Mako mai zuwa za su sake karawa a wasa na biyu

Kungiyar kwallon kafa ta Arsenal ta tashi wasa babu ci da Besitas a wasan farko na share-fagen shiga gasar cin kofin zakarun Turai a Turkiya.

Dan kwallon Arsenal Aaron Ramse ya karbi jan kati a minti na 79, yayin da kungiyar ke fafutukar zura kwallo a raga.

Daf ya rage Alex Oxlade-Chamberlain dan wasan Arsenal ya zura kwallo a raga, shi ma dan wasan Besiktas Demba Ba ya kai kora inda kwallon da ya doka ta bugi turke.

Sauran sakamakon wasannin da aka fafata FC Copenhagen ta Denmark ta yi rashin nasara har gida a hannun Bayer 04 Leverkusen ta Jamus da ci 2 - 3.

Wasa tsakanin Napoli ta Italy da Athletic de Bilbao ta Spaniya tashi suka yi kunnen doki, FC Steaua Bucuresti ta Romania ta doke Ludogorets Razgrad ta Bulgaria da ci daya mai ban haushi.

Kungiyar Red Bull Salzburg ta Austria ta doke Malmö FF ta Sweden da ci 2 : 1.

Za su buga wasa na biyu ranar laraba 27 ga watan Agusta.