Derek Boateng ya koma SD Eibar ta Spain

Derek Boateng Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Derek Boateng ya ce zai yi wasa tukuru a SD Eibar

Dan kwallon Ghana mai buga wasan tsakiya Derek Boateng, ya kammala koma wa kulob din SD Eibar da ke Spain.

Dan wasan mai shekaru 31 da haihuwa, ya bugawa Ghana gasar cin kofin Duniya a shekarar 2006 da 2010, wanda ya koma SD Eibar bayan da kwantiraginsa ya kare da kulob din Rayo Vallecano.

Boateng bai bugawa Rayo tamaula ba tun lokacin da ya koma kungiyar daga kulob din Fulham a watan Yuni.

Dan kwallon ya ce "Ya yi farin ciki da zai buga gasar cin kofin La Liga ta Spaniya a bana".

Ya kara da cewa "Sabuwar kungiyar na da jan aiki a gabanta, domin kauracewa faduwa daga gasar".