Mourinho: Ban son Cech ya bar mu

Peter Cech Hakkin mallakar hoto epa
Image caption Watakila golan ya bar Chelsea a kakar wasan bana

Jose Mourinho ya ce baya fatan mai tsaron ragarsa Petr Cech, zai bar kulob din Chelsea, duk da rashin saka shi a karawar da suka doke Burnley da ci 3-1 ranar Litinin.

Chelsea ta yi amfani da Thibaut Courtois mai shekaru 22 da haihuwa a matsayin gola a karawar, bayan da ya dawo kungiyar daga kulob din Atletico Madrid da aka bayar da shi aro tsawon shekaru uku.

Mourinho ya ce "Ina fatan babu wata kungiya dake zawarcin dan wasan, idan ma da akwai ya ki amincewa da su, ban son ya bar buga mana wasa".

Cech, mai shekaru 32, shi ne golan Chelsea tun daga shekarar 2004.

Chelsea ta dauko dan kwallon daga kungiyar Rennes ta Faransa a watan Fabrairun 2004, amma sai a watan Yuli ya koma Stamford Bridge.

Dan kasar Czech ya lashe kofunan Premier uku da kofin zakarun Turai Champion League da kofin Europa.