Suarez: Ba zan sake cizon kowa ba

Luis Suarez Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Dan wasan ya yi alkawarin ba zai sake cizon kowa ba

Sabon dan kwallon Barcelona Luis Suarez ya ce ya tattauna da kwararre masanin halayyar dan Adam, wanda ya ja masa kunne kar ya kara yin cizo a filin wasa.

Suarez na zaman hukuncin dakatarwar watanni hudu, bayan da aka same shi da laifin cizon dan kwallon Italiya Giorgio Chiellini a gasar kofin Duniya, kuma laifi na uku da ya yi cizo lokacin wasa.

Dan wasan ya yi alkawari ga magoya bayansa cewa "Su kwantar da hankalinsu ba zai sake cizon kowa ba a fili".

Suarez, mai shekaru 27 dan kwallon Uruguay ya ce, hankalinsa ya kadu matuka da laifin cizon da ya aikata a Brazil, sai dai ya daukaka karar dakatar da shi da aka yi a kotun daukaka kara ta wasanni ta Duniya.

Kotun ta tabbatar masa da laifinsa na dakatar da shi wasanni hudu har zuwa cikin watan Okokoba, amma zai iya buga wasan atisaye da yi wa kamfanoni talluka.