CAF: Kila Ivory Coast ta fuskanci fushi

Ebola Fear Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Idan har Ivory Coast ba ta buga wasan ba, Caf za ta hukunta ta

Karawa tsakanin Ivory Coast da Saliyo a wasan neman tikitin shiga gasar cin kofin Nahiyar Afirka ya zama kila wa kala sakamakon dokar hana shiga wasannin kasa da kasa da kasar Ivory Coast ta yi.

Hukumar lafiya da kuma ta wasanni ne suka yanke hukuncin haka don tsoron kamuwa da cutar Ebola ranar Talata.

Ivory Coast ce ya kamata ta karbi bakuncin Saliyo ranar 6 ga watan Satumba, a karawar wasan farko na cikin rukuni.

Har yanzu ba a samu labarin bullar Ebola a Ivory Coast ba, illa barkewar cutar a makwabtanta da suka hada da Guinea da Liberia da Saliyo da kuma Najeriya.

Har yanzu ba bu tabbacin ko Ivory Coast za ta karbi bakuncin wasan ko kuma shirin neman filin da ya kamata su fafata.

Idan har Ivory Coast bata yarda ta buga wasan ba, za ta iya fuskantar hukunci daga hukumar wasan kwallon kafa ta Afirka CAF.