Dzeko ya sabunta kwantiraginsa da City

Edin Dzeko Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Dzeko ya ce da sauran gudunmawa da zai bai wa City

Edin Dzeko ya tsawaita kwantiraginsa da kulob din Manchester City zakarar kofin Premier har zuwa tsawon shekaru hudu.

Dan wasan mai shekaru 28 ya bi sawun 'yan wasan da suka tsawaita kwantiraginsu da kulob din da suka hada da Samir Nasri da Aleksandar Kolarov da Vincent Kompany da kuma David Silva.

Dzeko ya ce "Sama da shekaru uku da rabi mun kafa tarihi a kungiyar, har yanzu da sauran gudunmawar mahimmiya da zan kara bayar wa".

Ya kara da cewa " Manchester City gida ne a wajensa, sannan yana jin dadin buga tamaula a kungiyar.