Man United ta dauko Marcos Rojo

Marcos Rojo Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Dan wasan ya ce ya yi murnar komawa United kwallo

Kulob din Manchester United ya bada sanarwar daukar dan wasan Argentina mai tsaron baya Marcos Rojo kan kudi fam miliyan 16 a kwantiragin shekaru biyar.

Dan kwallon mai shekaru 24, ya koma United ne da musayar Nani, wanda zai koma Sporting Lisbon wasa aro tsawon shekaru da dama.

Rojo wanda zai saka taguwa mai lamba biyar a United ya ce "Bugawa babbar kungiya kwallo shi ne fatansa, inda mafarkinsa ya zama gaskiya".

Dan kwallon ya bugawa Argentina wasanni biyar a gasar cin kofin Duniya da Brazil ta karbi bakunci, wanda kasar ta kai wasan karshe.

Manchester United ta dauko 'yan kwallo uku kenan a kakar wasan bana.