Real Madrid ta musanta raunin Ronaldo

Cristiano Ronaldo Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Real Madrid ta ce raunin da ya ji bai kai ya kawo ba

Kungiyar Real Madrid ta ce raunin da Cristiano Ronaldo ya ji a karawar da suka yi da Atletico Madrid a gasar Super Cup na Spaniya bai kai ya kawo ba.

An sauya gwarzon dan kwallon Duniyar mai shekaru 29 a wasan inda James Rodriguez ya shiga fili a madadinsa.

Kocin Madrid Carlo Ancelotti ya ce "Dan wasan ya samu buguwa a bayansa, inda ya dinga jin radadi, likitoci ne za su duba shi sannan su tabbatar da girman raunin".

Ronaldo ya buga gasar kofin Duniya duk da rauni a gwiwa da cinyarsa, wanda kasarsa Portugal ta kasa kai wa zagaye na biyu ba gasar.