CAF za ta saurari daukaka karar Rwanda

Rwanda appeal
Image caption CAF ce ta kori Rwanda daga wasan neman tikitin shiga gasar kofin Nahiyar Afirka

CAF za ta saurari daukaka karar da Rwanda ta shigar gabanta ranar 27 ga watana Agusta, saboda korarta da aka yi daga wasan neman tikitin shiga gasar cin kofin Afirka.

CAF, ta kori Rwanda ne daga wasannin neman tikitin shiga gasar cin kofin Afirka saboda samunta da laifin yin amfani da dan wasa Daddy Birori wanda shekaru da sunansa suka banbanta a passport dinsa.

Congo ce ta shigar da korafin da aka kori Rwanda daga gasar, bayan da ta mika shaidun da ke nuna cewa dan wasan yana amfani da sunaye biyu da shekaru daban-daban a passport dinsa.

Dan wasan mai suna Birori, yana kuma amsa sunan Etakiama Agiti Tady a kulob din AS Vita na Congo.

Kocin Rwanda Stephen Constantine ya shaidawa BBC cewa "Ba mu samu cikakken bayani dangane da dan wasan ba, domin haifaffen Congo ne, amma shekaru biyar yana bugawa Rwanda tamaula".