Di Maria zai bar Real Madrid

Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Di Maria ya haskaka a gasar cin kofin duniya

Dan kwallon Argentina, Angel Di Maria ya bayyana wa Real Madrid cewar yanason ya bar kungiyar.

Ana tunanin Di Maria zai koma Manchester United, tun bayan da Louis van Gaal ya nuna sha'awar sayen dan kwallon mai shekaru 26.

Kocin Real Madrid, Carlo Ancelotti ya tabbatar da cewar dan wasan ya ki amince ya sabunta kwangilarsa tare da Real Madrid.

Ancelotti ya bayyana cewar "Di Maria ya ce yanason ya tafi kuma ya ki amincewa da tayin kulob din."

Di Maria ya koma Real Madrid ne daga Benfica a shekara ta 2010 a kan fan miliyan 20.

Karin bayani