Ghana ba ta gayyaci Essien tawagarta ba

Kwesi Appiah
Image caption Ghana za ta karbi bakuncin Uganda cikin watan Satumba

Kocin Ghana Kwesi Appiah ya bayyana sunayen 'yan wasa 24 da ya gayyato domin buga karawar neman tikitin shiga gasar cin kofin Nahiyar Afirka na badi.

Cikin tawagar babu mai tsaron raga Adam Kwarasey da dan kwallon Milan Michael Essien a wasan rukuni na hudu da za su fafata.

Black Stars za ta karbi bakuncin Uganda ranar 5 ga watan Satumba a Kumasi, daga baya ta kara da Togo kwanaki biyar tsakani.

Haka kuma kocin bai gayyaci Sulley Muntari da Kevin-Prince Boateng, wadan da aka kora daga tawagar kasar lokacin gasar cin kofin Duniya a Brazil saboda halin rashin da'a.

Ga sunayen 'yan wasan 24 da Ghana ta gayyata

Masu tsaron raga: Fatau Dauda (Chippa United, South Africa), Adams Stephen (Aduana Stars) da Razak Braimah (Mirandes FC, Spain)

Masu tsaron baya: Daniel Opare (FC Porto, Portugal), Harrison Afful (Esperance FC, Tunisia), Awal Mohammed (Maritzburg, South Africa), Baba Rahman (FC Augsburg, Germany), Jeffery Schlupp (Leicester City, England), John Boye (Erciyesspor FC, Turkey) da Jonathan Mensah (Evian FC, France)

Masu wasan tsakiya: Emmanuel Agyemang Badu (Udinese, Italy), Rabiu Mohammed (Krasnodar, Russia), Yusif Chibsah (Sassuolo, Italy), Kwadwo Asamoah (Juventus, Italy), Mubarak Wakaso (Rubin Karzan, Russia), Atsu Christian (Everton, England), Asante Solomon (TP Mazembe FC, DR Congo), Gyimah Edwin (Black Aces, South Africa), Afriyie Acquah (Parma FC, Italy) da Andre Ayew (Olympique Marseille, France)

Masu zura kwallo a raga: Asamoah Gyan (Al Ain, UAE), Jordan Ayew (Lorient, France), Abdul Majeed Waris (Spartak Moscow, Russia), David Accam (Helsenborg, Sweden),