Liverpool ta yarda da farashin Balotelli

Mario Balotelli
Image caption Tuni dan wasan ya yi ban kwana da magoya bayansa

Kulob din liverpool ya amince da farashin dan kwallon AC milan Mario Balotelli, kan kudi fam miliyan 16 domin komawa kungiyar.

Kocin Liverpool Brendan Rodgers na son dan kwallon Italiyan ne mai shekaru 24, domin ya karfafa 'yan wasansa da ke zura kwallo a raga.

Balotelli ya koma Milan ne daga Manchester City kan kudi fan miliyan 19 a kakar wasan bara, ya buga wasanni 54 a gasar Serie A ya kuma zura kwallaye 30.

Har yanzu kungiyoyin biyu suna tattaunawa kafin su rattaba hannu a kwantiragi, amma tuni Balotelli ya yi ban kwana da kasar Italiya.

Milan ta sanar a shafinta na Intanet cewa "Mario Balotelli ya bar Milanello da tsakar ranada ya yi ban kwana da 'yan wasan kulob din".