Takaddama kan zaben NFF

Aminu Maigari Hakkin mallakar hoto getty
Image caption Mako biyu tsakanin taron hukumar za a gudanar da zabe

Hukumar kwallon kafar Nigeria (NFF) ta yi kira da a kauracewa jawabin da shugaban kwamitin zaben hukumar Mr Amoni Biambo ya yi da cewar za a kada kuri'ar zaben sabbin shugabanni ranar 26 ga watan Agusta a Warri jihar Delta.

Hukumar ta ce an samu kuskure ne, amma kamar yadda ta tsara ranar Talata 26 ga watan Agusta za ta gudanar da babban taronta wanda zai tsaida ranar da za a zabi sabbin shugabannin hukumar da za su yi jagorancin shekaru hudu.

Sakatare janar na hukumar NFF Barr. Musa Amadu ya ce "Hukumar kwallon kafar NFF ce za ta tsaida ranar zabe a lokacin babban taronta, da ba zai wuce mako biyu tsakani ba, saboda haka za a gudanar da zaben hukumar a farkon watan Satumba".

Hukumar kwallon kafa ta Duniya FIFA ta goyi da bayan shirin taron NFF ya fidda ranar da za a gudanar da zaben shuwagabanni da za su jagoranci hukumar, in ji mai magana da yawun NFF Ademola Olajire.

A wasikar da FIFA ta rubutawa shugaban hukumar kwallon kafa Najeriya Aminu Maigari dauke da sa hannun sakatare janar dinta Markus Kattner ta ce "Ta goyi bayan cewa taron hukumar ya fitar da ayyukan kwamitin zabe da kafa kwamitin sauraren korafi da shigar da kara".

FIFA, ta kuma mika jajenta ga hukumar kwallon kafa ta NFF bisa gobarar data kama ginin hukumar dake Abuja ranar Laraba.

Sai dai kwamitin zaben NFF ya ce babu abinda zai hana gudanar da zaben hukumar a ranar 26 ga watan Agustan.