U20: Nigeria ta lallasa Koriya ta Arewa

Hakkin mallakar hoto NFF
Image caption Falconets ta fitar da Afrika daga kunya

Tawagar Nigeria ta tsallake zuwa wasan karshe a gasar cin kofin mata ta 'yan kasa da shekaru 20, bayan ta lallasa Koriya ta Arewa da ci 6 da 2.

'Yar Nigeria Asisat Oshoala ce ta zura kwallaye hudu a wasan zagayen kusada karshe da aka buga a ranar Laraba a New Brunswick da ke Canada.

Sauran 'yan Nigeria da suka zura kwallo sun hada da Courtney Dike da kuma Uchechi Sunday.

Ri Un-Sim da kuma Jon So-Yonn ne suka ci wa Koriya ta Arewa kwallayenta.

Nigeria za ta kara da Faransa ko Jamus a wasan karshe a ranar Lahadi a birnin Montreal.